Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Himalaya
Wani yankin tsaunuka ne dake a nahiyar
Asiya
. Karshen Himalaya daga yamma yana a kasar
Pakistan
. Tsaunukan sun shiga ne ta
Jammu da Kashmir
, Himachal Pradesh , Uttaranchal, Sikkim da
Arunachal Pradesh a yankin Kasar
Indiya
, Nepal , da Bhutan. Karshen sa daga gabashi yaje har
Tibet
. Sun rabu zuwa yankuna 3 Himadri, Himachal da Shiwaliks. Tsaunuka 15 mafiya tsawo a
duniya
na a Himilaya. Daga ciki akwai tsaunukan Mount Everest, K2 , Annapurna, da Nanga Parbat . Mount Everest shine mafi tsawon tsauni a duniya da tsawon mita 8,849. Daga cikin dogayen tsaunuka mafiya tsayi a duniya Tara na a yankin Himalayan
Nepal
. Kalmar "Himalaya" na nufin
gidan kankara
da yaren Sanskrit, tsohon yaren
Indiya
. Tsaunukan Himalaya sune suka raba al'adun
Sinawa
da
Indiyawa
na tsawon lokaci. Da yaren Sanskrit, tsohon yaren
Indiya
. Tsaunukan Himalaya sune suka raba,wanda yagano himalayas a shekarar Alib
1733
,Shine wani masanin yanayin da yasha fa Duniya(Jean-Baptiste),Dan kasar francar ne,Save
Open…
Zoom image…
179x127
4.4 kB JPEG.
Himalaya waje ne da yayi kaurin suna sosai a tsakankanin yan yawon bude ido da shakatawa sabo da albarkar yanayin da ke akwai na gandun daji. daga cikin tsirrai da bishiyoyin dake akwai sun hada da Oak, Pine, Fir,
Rhododendron , Birch, Juniper,da Deodar. Ire iren
dabbobin
da ke akwai a sassan dazuzzukan Himalaya sun hada da
damusa
, Shidiyar
Tinkiya
,
Giwa
,
Kada
da
Kura
. A yankin kudancin Himalaya kinda akwai yanayin Sanyi sosai, dabbobi basu cika zama a wuraren ba. Haka kuna su wadanda ma keep rayuwa a wuraren, lokacin sanyi sukanyi hijira zuwa yankunan da sanyin ke da sauki.
Wasu daga cikin guraren gandun daji masu jan hankali
- Jim Corbett National Park
- Namdhpha National Park
- The Royal Chitwan Park
- Kaziranga National Park
- Royal Bardia National Park
- Great Himalayan National Park