Intanet ko Yanar gizo: Ta kuma kasan ce wani irin tsari ne na harhade-harhaden na'urorin duniya a bisa bangare guda domin sadar da junansu a bisa dogon zango ba tare da hadakar waya a tsakani ba (wireless). Biliyoyin na'urorin computa ne ke jone da juna a babban turken internet a duniya .
Tasirin intanet kan rayuwar Yan'adam dai fasaha ce da wasu masana ke cewa ta sauya fasalin yadda ake gudanar al'amuran rayuwa a duniya gaba daya, har ta kai wasu na cewa sun fara mantawa da ko yaya rayuwa take kafin zuwan Intanet. [1]