한국   대만   중국   일본 
Kofa:Kimiyya - Wikipedia Jump to content

Kofa:Kimiyya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kofa:Kimiyya
Wikimedia portal (en) Fassara
Dr. Wendy Bohon a cikin ?akin gwajin kimiyya
Ma auni
ma auni ne na ilimin kimiyya

Kimiyya na nufin ilimin zahiri da ake iya ganin sa, ko ta?a shi, ko ?an?anonshi, da kimiyya ne ake samar da Fasaha. [1] kimiyya dabaru ne a fannin ilimin lissafi, ilimin ?wayar halitta da ilimin na'ura wajen samar da rayuwa mai sau?i a fannin Sifiri , Lafiya , Makamai , Noma , Lantarki , Na'ura da Gini . Kimiyya ce take samar da Fasaha a ?wa-?walwan Mutane har su ?ir?iri sa babbin abubuwa. Duk ci gaban da aka samu a Duniya to a dalilin Kimiyya ne, kuma kimiyya ce ta ke dun?ule ilimi dayawa waje guda kuma ta raba su a matsayin ilimi mai zaman kanshi. [2] Asalin ilimin Kimiyya ya samo asali ne a ?asar Misra wato Egypt da kuma Mesopotamia a shekaru 3500 zuwa shekara ta 3000 BCE kafin zuwan Annabi Isah . Sun bayar da gudummawa a fannoni daban-daban kamar su ilimin Lissafi , Ilimin Taurari da Ilimin Magunguna . wannan kimiyyar ya shiga har izuwa girka wato ( Greek) da daular Rumawa, ya wayar musu da kai. Ilimin Kimiyya na girkawa ya ?arfafa ma 'yan gabashin Turai kuma ya wayar musu da ido a shekara ta (400 zuwa 1000 CE) amman a lokacin ba ai amfani da shi a Duniyar Musulmi ba, sai daga baya a lokacin Islamic Golden Age . A lokacin ne Musulmai sukayi bincike a gabashin nahiyar Turai daga ?arni na 10th zuwa ?arni na 13th. Kimiyya ta ratsa ko inane a ?arni na 19, wanda a lokacin ne aka samar da gwanaye a fannin Kimiyya har suka canza mata suna daga "natural philosophy" zuwa "natural science." [3]

Fannonin kimiyya [ gyara sashe | gyara masomin ]

Kimiyya ta zamani ta kasu zuwa kaso uku ne, sune kamar haka:-

A daa can ana samun ilimin kimiyya ne a gun sanannun masu ilimi da kuma bincike dan ?ir?irar sabuwar Kimiyya ko gano ta. Amman a wannan zamanin ana samun ilimin Kimiyya ne ka?ai a Jami’o’i da ?ananan cibiyoyin Ilimi kuma ana sayar da kimiyyar ne zuwa ga kamfanoni da masana’anta domin ci gaba da samun arzi?i.

Koyon Wikipedia
Ajin karatu | Manufofin Wikipedia | Saka Fayal | Editin | Editocin Hausa Wikipedia | Tambaya | Bidiyon koyo
  1. https://www.britannica.com/science/science
  2. https://www.dictionary.com/browse/science
  3. https://hausa.legit.ng/1086886-kimiya-ta-bayyana-hanyoyin-3-da-iya-kawo-karshen-duniya.html