Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Khula'hur-Rashidun
(a Larabci, Khilafa-al-Raahidah
??????? ???????
) Sune Kalifofin farko guda hudu ko kuma magada na jagorancin Daular Musulunci tun bayan Wafatin fiyayye halitta Annabi Muhammad (s.a.w) a shekara ta 632M wato 11H. Khulafa'ar-Raahidun sune sukayi shugabancin Daular
Musulunci
daga 632-661M. Musulmai mabiya Sunnah wato
Sunni
Islam ne ke kiran su da sunan Khulafa'hur-Rashidun, amma a bangaren mabiya
Shi'a
wannan kalmar bata amfani domin kuwa sun hakikance da Kalifofin ukun farko kafin Sayyadina Ali sunyi kwace ne, kuma basa ganin su da girmamawa.
Khulafa'hur-Rashidun sunyi kalifanci ne na shekara 25
Taswirar daular Khulafa'hur-Rashidun
Bayan Wafati Annbi (s.a.w) ne sahabban sa suka fara tattaunawa game da ko wanene zai gaje shi wajen jagorancin musulmai a yayinda sukuma iyalan gidansa suna can suna shirya Janazar sa. Sayyadina Umar da Abu Ubaidullah ibn al-jarrah suka nuna mubaya'ar su ga Sayyadina Abubakar.
thumb taswirar daular kalifofi hudu mai baiyana fadadar daular tun daga kalifan farko
Bayan Wafatin Annabi
Muhammad
(s.a.w) a shekarar 632 miladiyya, sai Mutanen
Madina
(
Ansar
) suka fara tattaunawa akan wanene zai gaji Kalifancin
Musulmi
a tsakanin su. Sai suka zabi
Sayyadina Abubakar
ya zama kalifa na farko na
Musulunci
. Daganan sai shi kalifan na farko yaci gaba da jan ragamar Musulmai da aiwatar da al'amuran Musulmi da yada addini tsakanin kasashen makabta na larawa da sauran kabilu. Tsarin Kalifanci baya nufin sarauta, tun daga Kalifan farko har na karshe basa daukar kansu a matsayin sarakuna. Domin Kalifanci na nufin
Jagorancin Annabta
(ma'ana jaogoranci na al'amuran musulmi kwatankwacin na annabta).
Kalifofin da suka biyo bayan kalifan farko sune,
Sayyadina Umar
, wato kalifa na biyu, sai
Sayyadina Usman
, kalifa na Uku, sai
Sayyadina Aliyu
, kalifa na hudu. Daganan kuma kalifanci ya kare sai sarauta.