Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
![](//upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/9/99/Question_book-new.svg/51px-Question_book-new.svg.png) |
Wannan mukalar bata da
Reference (Manazarta)
ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da
Reference (Manazarta)
a cikin wannan mukalar.
![](//upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/e/e7/DiaryQuill_icon.svg/40px-DiaryQuill_icon.svg.png) .
|
muryar Aike Soyinka
hoton Wole Soyinka
Wole Soyinka
Akinwande
Oluwole Babatunde Soyinka(
Yarbanci: Akinwande Oluwo?le Babatunde S?oyiinka; an haife shi ne a ranan 13 ga watan Yulin shekara ta 1934), wanda aka sani da Wole Soyinka (lafazin [w?le ?oj?nka]), ?an wasan kwaikwayo ne na
Nijeriya
,
mawa?i
kuma
marubuci
. An ba shi lambar yabo ta
Nobel
ta adabi a shekara ta 1986, mutum na farko a sub-saharan Africa da aka girmama a wannan rukunin. An haifi Soyinka a cikin dangin Yarbawa a Abeokuta. A 1954, ya halarci Kwalejin Gwamnati a
Ibadan
, sannan ya halarci Kwalejin Jami'ar Ibadan da Jami'ar Leeds a
Ingila
. Bayan ya yi karatu a Najeriya da
Ingila
, ya yi aiki tare da gidan wasan kwaikwayo na Royal Court da ke
Landan
. Ya ci gaba da rubuta wasannin kwaikwayo wa?anda aka samar a ?asashen biyu, a gidajen kallo da rediyo. Ya taka rawar gani a tarihin siyasar
Najeriya
da gwagwarmayar neman 'yanci daga
Burtaniya
. A shekarar 1965, ya kwace gidan watsa labarai na Yammacin Najeriya ya watsa shirye-shiryen neman a soke zaben yankin Yammacin Najeriya. A shekara ta 1967, a lokacin ya?in basasar
Najeriya
, gwamnatin tarayya ta Janar
Yakubu Gowon
ta tsare shi tare da sanya shi a
kurkuku
na tsawon shekaru biyu.