A ranar 14 ga watan Afrilu, 2014 da misalin ?arfe 6:45 na safe, wasu bama-bamai biyu sun tashi a wata tashar mota mai cunkoson jama’a, a garin Nyanya na
Jihar Nasarawa
, hakan ya jawo mutuwar mutane a?alla 88 tare da jikkata wasu 200. Tashar motar na da nisan kilomita 8 ne daga kudu maso yammacin
babban birnin tarayya
.
[1]
[2]
[3]
[4]
[5]
Kungiyar Boko Haram
ta ?auki alhakin kai harin kwanaki shida bayan faruwar lamarin. Hakan ya faru ne sa'o'i ka?an kafin a sace ?an matan Chibok.
Wasu bama-bamai da aka ?oye a cikin motoci sun tashi da sanyin safiya a wata tashar mota da ke Nyanya a wajen
Abuja
. Bayan fashewar farko, an sake samun tashin bama-bamai yayin da tankunan mai a cikin motocin da ke kusa da su suka tarwatse.
[6]
Abbas Idris, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a Abuja, ya tabbatar da mutuwar mutane 71 tare da jikkata wasu 124.
[7]
Tashar motar na yi wa talakawa da wasu ?abilu ko mabiya wani addini, hidima.
[4]
Kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa, Manzo Ezekiel, ya tabbatar da cewa da yawan wa?anda suka jikkata na samun kulawa a asibiti.
[7]
Ya zuwa ranar 15 ga watan Afrilu, adadin wa?anda suka mutu ya karu zuwa 75, yayin da masu bincike ke ci gaba da za?ulo tarkacen da aka samu a wurin da fashewar ta afku.
[1]
Har wayau ya zuwa ranar 18 ga watan Afrilu, adadin wa?anda suka mutun ya ?aru zuwa 88, yayin da fiye da 200 aka ruwaito sun jikkata.
[5]
Kungiyar Boko Haram
ta ?auki alhakin kai harin, kwanaki shida bayan faruwar lamarin?a cikin bidiyon da ya nuna su a lokacin da su ke ?aukar alhakin kai harin, ya kunshi shugaban kungiyar
Abubakar Shekau
wanda aka saki a ranar 19 ga watan Afrilu.
[8]
Hukumar ?an sandan kasa da kasa ta Interpol ta kama Aminu Sadiq Ogwuche a kasar
Sudan
a watan Mayun 2014, bisa zargin kasancewar sa a cikin ?aya daga cikin wa?anda su ka kai harin bam ?in.
[9]
Sa'o'i kadan biyo bayan harin, ?an ?ungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da ?aruruwan ?an matan makarantar
Chibok
.
Shugaban Najeriya
Goodluck Jonathan
ya ziyarci wurin da fashewar ta faru, inda ya ce:
Mun yi asarar adadi mai yawa. Muna jajantawa ?asar mu, maza da mata. Batun Boko Haram wani mummunan tarihi ne a cikin wannan lokaci na ci gabanmu. Gwamnati na yin komai don ganin mun ciyar da ?asarmu gaba. Amma wa?annan abubuwan da ba dole ba ne ke jawo mana koma baya. Amma za mu kawo karshen hakan.
[10]
Harin dai ya zo ne kwana guda bayan ?an majalisar dattawan Najeriya
Ahmed Zanna
ya yi ikirarin cewa ?ungiyar ?an ta'addan, ta hallak fararen hula 135 a arewa maso gabashin
Najeriya
a wasu jerin hare-hare uku da aka kai, a makon da ya gabata.
[11]
Coordinates
:
9°03′00″N
7°30′00″E
/
9.0500°N 7.5000°E
/
9.0500; 7.5000