한국   대만   중국   일본 
Fatima - Wikipedia Jump to content

Fatima

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fatima
Rayuwa
Haihuwa Makkah , 27 ga Yuli, 604
?asa Khulafa'hur-Rashidun
Harshen uwa Larabci
Mutuwa Madinah , 14 Disamba 632
Makwanci Al-Baqi'
?an uwa
Mahaifi Muhammad
Mahaifiya Khadija Yar Khuwailid
Abokiyar zama Sayyadina Aliyu
Yara
Ahali Ummu Kulthum , Rukayyah , Zainab yar Muhammad , Ibrahim ?an Muhammad , Yaran Annabi da Abdullahi ?an Muhammad
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a maiwa?e
Imani
Addini Musulunci

F??ima bint Mu?ammad ( Larabci : ???????? ?????? ???????? ‎ , 605/15?632 CE), wanda aka fi sani da F??ima al-Zahr?? ( ???????? ??????????? ), ta kasance diyar annabin musulunci Muhammad da matarsa Khadija . [1] Mijin Fatima shi ne Ali , shine na hudu a cikin Khalifofin Rashidun kuma Imamin Shi'a na farko . 'Ya'yan Fatima su ne Hasan da Husaini Imaman Shi'a na biyu da na uku. [2] [3]

An kwatanta Fatima da Maryamu mahaifiyar Isah , musamman a aqidar Shi'a. [4] [5] An ce Muhammadu ya dauke ta a matsayin mafificiya a mata [2] [6] kuma mafi soyuwa a gare shi. [7] [2] Sau da yawa ana kallonta a matsayin babban abin tarihi ga matan musulmi da kuma ita me tausayi, karimci, da jurewa wahala. [4] Ta hanyar Fatima ne zuriyar Muhammadu suka wanzu har yau. [8] [6] Sunanta da lakabinta sun kasance sanannen za?i ga 'yan mata musulmai. [9] [10]

Lokacin da Muhammadu ya rasu a shekara ta 632, Fatima da mijinta Ali sun ?i amincewa da mulkin k halifa na farko, Abubakar . Ma'auratan da magoya bayansu sun yi imanin cewa Ali shi ne mafi cancantar magajin Muhammadu, [4] mai yiwuwa suna nufin sanarwarsa a Ghadir Khumm . [11]

Rigima ta kunno kai dangane da mutuwar Fatima a cikin watanni shida da mutuwar Muhammadu. [8] Ahlus Sunna sun yarda cewa Fatima ta rasu ne da bakin ciki. [3] A cikin Shi’a kuwa, an ce mutuwar Fatima (barin da tayi) ta yi ne kai tsaye sakamakon raunukan da ta samu a lokacin wani farmaki da aka kai gidanta don murkushe Ali, wanda Abubakar ya umarta. [2] An yi imanin cewa fatawar Fatima da ta rasu shi ne kar khalifa ya halarci jana’izarta. [12] [13] An binne ta a asirce da daddare kuma ba a tabbatar da ainihin inda aka binne ta ba. [14] [15]

Suna da la?abi [ gyara sashe | gyara masomin ]

Mafi sanannan la?abinta shi ne al-Zahra ( lit. 'me haskakawa', 'me haske?' ), [2] wanda ke nuni akan taqawarta da tsayuwarta a cikin addu'a. [16] Shi'a sun yi imani da wannan taswirar cewa tana nuni ne ga halittarta ta farko daga hasken da ke ci gaba da haskakawa a cikin halittu. [2] Shi'a Ibn Babawahy ( d.?991 ) ya rubuta cewa, duk lokacin da Fatima ta yi addu'a, haskenta yana haskakawa ga mazauna sama kamar yadda hasken taurari ke haskaka mazaunan duniya. [7] Sauran lakabin ta a cikin Shi'a su ne al-Shiddiqa ( lit. 'me gaskiyta?' ), [10] al-Tahira ( lit.?'me tsarki' ), [1] al-Mubaraka ( lit.?'me albarka' ), [1] da al-Mansura ( lit.?'wanda Allah ya taimaka' ). [2] Wani lakabin Shi'a kuma shi ne al-Mu?additha, bisa la'akari da rahoton cewa mala'iku sun yi magana da Fatima a lokuta da dama, [17] [18] [19] kamar Maryamu mahaifiyar Isah . [18]

Manazarta [ gyara sashe | gyara masomin ]

  1. 1.0 1.1 1.2 Campo 2009a .
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 2.5 2.6 Buehler 2014 .
  3. 3.0 3.1 Veccia Vaglieri 2022a .
  4. 4.0 4.1 4.2 Fedele 2018 .
  5. Ernst 2003 .
  6. 6.0 6.1 Qutbuddin 2006 .
  7. 7.0 7.1 Soufi 1997 .
  8. 8.0 8.1 Abbas 2021 .
  9. Amir-Moezzi & Calmard 1999 .
  10. 10.0 10.1 Rogerson 2006 .
  11. Amir-Moezzi 2022 .
  12. Mavani 2013 .
  13. Kassam & Blomfield 2015 .
  14. Khetia 2013 .
  15. Klemm 2005 .
  16. Ruffle 2011 .
  17. Aslan 2011 .
  18. 18.0 18.1 Ayoub 2011 .
  19. Pierce 2016 .