한국   대만   중국   일본 
Jima - Wikipedia

Jima hanya ce da ake sarrafa fata a gyara ta don a yi wani amfani na daban da ita, ko kuma jima sana'a ce ta gyara fatar dabba ta hanyar ciccire gashin jikin fatar da sauran abubuwan da ba'a so. Jima a kasar Hausa ta kasu kashi biyu, akwai na gargajiya sannan kuma akwai ta zamani. [1]

Jima
process (en) Fassara
Bayanai
?aramin ?angare na leather production process (en) Fassara, craft (en) Fassara da cleaning (en) Fassara
Bangare na Musulunci
Product or material produced or service provided (en) Fassara leather (en) Fassara
Intangible cultural heritage status (en) Fassara Living traditions ? An inventory of intangible cultural heritage in Sweden (en) Fassara
Shafin yanar gizo levandekulturarv.se… da levandekulturarv.se…
Gudanarwan tanner (en) Fassara
Uses (en) Fassara fata
turmin da akeyin jima

Aiki gyara sashe

Masu jiman zamani kuma sukan yi aikin fatu ta hanyoyin zamani don yin jakunkuna da takalma da rigar kujerun zama da kuma ita kanta fatar a kan gyarata don sayarwa ga sauran ?asashe. [2]

Ana iya amfani da fatar kowacce dabba wajen jima a nan kasar Hausa, a nan kasar Hausa an fi amfani da fatun kada da jimina da macizai da fatun awaki da tumakai da sauransu.

Jimar gargajiya ta kumshi mutanen da suke sarrafa fata su juya ta zuwa nau’i daban?daban wanda suke dunka layu da bante da rigar wuka (kube) da jakunkunan fata da linzami da takalmi da sirdin doki da sulke na fata.

Yadda ake Jima gyara sashe

Jima sana’a ce ta gyaran fata, wadda ake ciccire gashi da sauran abubuwan da ba a bukata daga jikin fata, a mayar da ita fes, domin yin wani abin amfani da ita. Masu yin wannan sana’a su ake kira Majema. Haka nan, gurin da ake yin wannan sana’ar ma a kan kira shi da sunan Majema.

 
jemammiyar fata

Asalin sana'ar Jima gyara sashe

Sana’ar jima sana’a ce da aka same ta a wurin Larabawa , an samu wannan sana’a a kasar Hausa can lokutan baya da Larabawa ke zuwa fatauci. Daga cikin irin wadannan masu zuwa fataucin akwai malamai masu karatun Alqur’ani, cikinsu kuwa akwai wadanda ke sarrafa fata domin yin shimfida wadda ake kira buzu, da kuma yin jaka wadda ake kira gafaka domin adana Alqur’ani da sauran takardun karatu. Zuwan su kasar Hausa sai ya zama suna koyawa almajiransu irin wadannan sana’o’i bayan karatu da suke koya musu. Wannan shi ne asalin samuwar wannan sana’a ta jima a kasar Hausa.

Kayan Aiki gyara sashe

Kayan aikin Jima sun hada da:

  1. Majema : Shi ne asalin gurin da ake gudanar da sana’ar jima. A nan ake yi mata komai.
  2. Kwatarniya : Mazubi ce da masu sana’ar ginin tukunya suke yi. A cikinta ake wanke fata da kuma jikata domin cire gashi da sauran abubuwa.
  3. Bagaruwa : Sinadari ce da ake cire gashin fata da ita.
  4. Toka da Kanwa : Su ne sidaran farko da ke rukar da gashin fata domin a cire shi daga jikin fata cikin sauki.
  5. Kashin Kaji/Tattabaru : Shi ne sinadari na biyu da yake rudar da sauran ?ananan gashi a jikin fata domin a cire shi cikin sau?i.
  6. Kartaji : Shi ne abin da ake tuje gashi da kuma nama daga jikin fata.
  7. Gwafa : Ana kafa ta domin daura igiyar shanya a jikinta.
  8. Igiya : Ita ake daura wa a jikin gwafa a shanya fata a kanta.
  9. Turmi : Kala biyu ne, akwai rabi wanda ake dora fata a jikinsa a tuje gashinta da kartaji. Sai kuma ainihin turmi wanda ake zuba fata a kir?a ta a ciki idan za a tura (idan za a yi mata launi) ta.
  10. Ta?arya : Da ita ake kir?a fata a cikin turmi.

Kartaji

Turmin da ake yin Gurza, Katsi da kuma Karni

Turmi da Ta?aryar Kir?i

Kayayyakin da Ake yi da Fata

Abu ne mai wahala a ?ididdige abubuwan da ake yi da fata bayan an jeme ta. Ka?an daga ciki akwai:

1. Sutura : Tun da can asali kuma har zuwa yau ?in nan ana amfani da fata wajen yin sutura. Suturar da ake yi da fata akwai riga, takalmi, hula, da majanyi (Belt), da sauransu. Kayan Kwalliya: Akan yi abubuwa da suka shafi kwalliya kamar irin su abin ma?alla makulli (key holder).

2. Jakakkuna : Ana yin jakakkuna manya da ?anana, irin na da da kuma na zamanin yanzu da muke ciki. Jakakkuna irin na da akwai gafaka (jaka ce da ake saka Al?ur’ani a ciki da sauran takardun karatu. Wannan na daga cikin tushen kawo wannan sana’a cikin ?asar Hausa), akwai burgami (jakar mafarauta), akwai zabira (jakar wanzamai), taiki (jaka ce mai kamar buhu da mutanen da ke amfani da ita wajen zuba kayayyaki kamar irin su hatsi da sauransu), sannan kuma akwai salka (ita ma jaka ce ta fata da ake zuba ruwa a ciki), da sauransu.

3. Kayan Ya?i da Farauta : Haka nan ana amfani da fata wajen yin kayayyakin ya?i da kuma farauta. Daga cikin irin wa?annan kayayyaki akwai: Warki (fata ce ake jeme ta iya tsawon dabbar, wacce mafarauta ke ratayawa a jiki domin samun kariya daga sara ko harbi. A wasu lokutan kuma akan bar ta da gashin nata sai dai a ?ame ta kawai. Sannan wasu sukan kira ta da buzu), sannan kuma akwai garkuwa (fata ce ta giwa da ake busar da ita sannan a ?amar da ita ta yi tauri, maya?a sukan kare harbin kibiya ko mashi da ita), akwai kube (kusan wata irin nau’in jaka ce da ake saka takobi, adda, ko wu?a a ciki. Wato gidan takobi, adda ko wu?a), akwai kuma safi, da ake sakawa a ?otar wu?a, takobi ko adda domin basu kariya daga tsagewa. Kayan ?ira: Ana yin kayan ?ira kamar zuga-zugi da fata. Kayan Ki?a: Da fata ake yin marufin mafiya yawan kayan ki?an gargajiyar Hausa, kamar irin su ganga, dundufa, kotso, kalangu, da sauransu.

4. Guga : Wata aba ce da ake ?ebo ruwa da ita daga cikin rijiya. Kayan fatake: Kilago, fata ce gyararriya da fatake ko maya?a ke amfani da ita wajen yin tanti a sahara ko daji.

5. Kayan Shimfi?a : Akwai buzu (fata ce akasari ta rago da malamai ke amfani da ita wajen yin shimfi?a idan za su yi karatu ko salla), akwai kuma tabarma ta zamani (Carpet), akwai kuma rigar fulo, da sauransu. ?afar Guragu.

Shanyar Fata

Kamalalliyar Fata

Amfanin Jima

Amfanin jima yana da yawa. Daga ciki akwai:

Samar da ayyukan yi. Ha??aka tattalin arzi?i. Samar da sutura. Yadda Ake Jima

Ana yin sana’ar jima a mataki-mataki kamar haka:

Ji?on Gashi: Matakin ji?o shi ne matakin farko da idan an kawo fata ake karka?e ta a wanke ta da ruwa domin cire abubuwan da ba a so da suka ha?a da ?asa ko gishiri. [3]

Sanwa: A wannan mataki ana samun ruwa ne a zuba a kwatarniya sannan a zuba toka, da kanwa da kuma katsi (tur?ayar gaurayen masu rini) a cikin ruwan sannan a zuba fatar a ciki. Wannan shi ne sanwa. Fata takan ?auki tsawon kwanaki biyu a kan sanwa. A wannan mataki gashi yake laushi wanda ko da hannu ma ana iya cisge shi.

 
 

Gurza: Gurza ita ce cire gashi daga jikin fata. A nan ana ?ora fata a kan turmi sai kuma a kawo kartaji a kankare gashin da ke jikinta. Kwaloko: Mataki ne da ake zuba ruwa ha?e da kashin kaji ko na tattabaru a cikin kwatarniya sannan a kawo fatar a zuba a ciki. Amfanin wannan shi ne cire ?an sauran gashin da ya rage. Katsi: Shi ne cire ?ananan gashin da ya rage a jikin fata. Ana yin katsi ne ta hanyar ?ora fata a kan turmi sannan a kankare ta da kartaji. Tsomi/Cu?a: Mataki ne da ake zuba ruwa a cikin kwatarniya sannan sai a samu bagaruwa a zuba a ciki, sai kuma a zuba fatar a ciki. Fata tana kwana ?aya a wannan mataki. Karni: Shi ne cire naman da ke jikin fata. Bayan an cu?e fata kuma sai a sake ?ora ta a kan turmi, a wannan karon kuma cikinta ake kankarewa domin fitar da sauran naman da masu fi?a suka rage. Yadda Ake Karni

Cu?a/Da?i: Cu?a ita ce zuba ruwa da bagaruwa a cikin kwatarniya bayan an yi mata karni. Fata takan ?auki kwana guda a cikin wannan ruwa.

Wanki: Ana zuba fata a cikin zallan ruwa a wanke ta. Shanya: Mataki ne da ake ?ora fata a kan igiya domin ta bushe. Launi: A wannan mataki ne ake yi wa fata launin da ake so, wanda ka iya zama ja, shu?i ko ruwan ?orawa. A wannan mataki ana yi wa fata abubuwa kamar haka: Shafa mangya?a. Ji?a fata da ruwa ta hanyar yayyafa ruwan a kan fatar. Kir?i: Mataki ne na launi da ake saka fata a turmi bayan an ji?a ta da ruwa a kir?a ta. Sai kuma a zuba kayan turi a launa fatar a cikin kwatarniya. Sai kuma a matse fatar daga ruwan turi. Sai a sake shanya ta a kan igiya. Ja: Mataki ne da ake ?ame fata da sauran danshinta na turi. Ana take gefen fata da ?afa sannan a ja ta a ?ame ta. Na?i: Mataki ne da ake na?e fatar a kifa biyu bayan an ?ame ta.

Diddigin bayanan waje gyara sashe

Alhassan A., Musa U.I., da Zarru? R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare.

Durumin Iya M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da ?ere-?eren Zamani a kan Sana'o'in Hausawa na Gargajiya. KABS Printing Services (NIG), Durumin Iya, Kano-Nigeria.

?walli K.M. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa (Babu sunan ma?aba'a).

Yakasai K. I. (Babu shekarar bugu). A San Mutum A Kan Cinikinsa (Babu sunan ma?aba'a).

Bibiliyo gyara sashe

Madauci, Ibrahim. (1968). Hausa customs . Isa, Yahaya., Daura, Bello. [Zaria]: Northern Nigerian Pub. Co. ISBN 978-169-097-6 .OCLC 489903061.

Manazarta gyara sashe

  1. "Yadda Sana'ar Sarrafa Fatar Dabbobi Ta Samu Karbuwa A Kamaru" . Aminiya.dailytrust.com. 18 March 2016 . Retrieved 6 January 2022 .
  2. Madauci, Ibrahim. (1968). Hausa customs . Isa, Yahaya., Daura, Bello. [Zaria]: Northern Nigerian Pub. Co. p.25-26. ISBN 978-169-097-6
  3. "Sana'ar Jima a ?asar Hausa" . rumbunilimi.com.ng. Archived from the original on 25 September 2021 . Retrieved 15 September 2021 .